<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><author>McGranahan, James (1840-1907), Whittle, Daniel Webster (1840-1901), Nathan, Elias (1840-1901)</author>
<lyrics>[V1]
 1) Dā ina zaune cikin duhuna,
 A cikin bautar zunubai.
 Ban sani Yesu yana sona ba,
 Ban kula da cetonsa ba.

[V2]
 KORUS
 Amma Allah ya ƙaunace mu,
 Ya ba da Ɗansa domin ya mutu,
 Don kada mu ma mu mutu
 Amma dai mu sami rai.

[V3]
 2) Shaiɗan ya ɗaure mini zuciyata
 A cikin halin hanyarsa.
 Ya hana mini hasken gaskiya
 Ya hana ni in bi Yesu.
 Korus

[V4]
 3) An kawo mana wa'azin ceto,
 An kawo mana gaskiya,
 Yesu ya kawar mini duhuna,
 Ya sa ni cikin hanyarsa.
 Korus

[V5]
 4) Yanzu jin daɗi kullum na ke yi,
 A cikin hanyar gaskiya.
 Na sami ceto daga zunubi,
 Rai na har abada.
 Korus

[V6]
 5) Sai wata rana Yesu za ya zo,
 Ya ɗauki dukan Masu Bi.
 Ni ma zan tafi can tare da shi,
 In zauna fa a gabansa.
 Korus</lyrics>
<title>Dā Ina Zaune Cikin Duhuna LW188</title>
<hymn_number>188</hymn_number>
</song>